Kafar watsa labaran Ma'an na Palastinu ya habarta cewa a safiyar yau Litinin dakarun HK Isra'ila sun kai farmaki a sansanin Addahisha na kudancin Baitu-laham dake yankin taken jodan, inda suka kashe wani Bapalastine guda tare da jikata wasu da dama na daban.
A jiya lahadi ma dakarun Isra'ila sun jikkata akalla palastinawa 4 a arewa, da gabashin yankin zirin Gaza.
Har ila yau, a ci gaba da farmaki da Sojojin Sahayuna ke kaiwa masu zanga-zangar neman dawo da hakki , a ranar juma'ar da ta gabata , Sojojin Isra'ila sun kashe Palastinawa 4 tare da jikkata wasu 210 na daban.
23 Yuli 2018 - 13:12
Lambar labari: 902771
A ci gaba da farmakin da Sojojin HK Isra'ila ke kaiwa sansanin yankin kogin jodan, wani Bapaltine ya yi shahada sannan wasu da dama sun jikkata.